30 Maris 2021 - 18:24
An Koma Zirga-Zirga A Mashigar Suez Bayan Janye Jirgin Ruwan Da Ya Toshe Hanyar Mashigar

Rahotanni sun bayyana cewar an dawo da zirga-zirga a mashigar nan ta Suez ta ƙasar Masar bayan da wani katafaren jirgin ruwan dakon kayayyaki ya toshe da kuma tokare hanyar wucewar sauran jiragen ruwan na kusan mako guda.

ABNA24 : Shugaban hukumar kula da mashigar ta Suez Admiral Osama Rabie ne ya sanar da dawo da zirga-zirgar bayan da aka samu nasarar janye jirgin ruwan ɗaukar kayan na ƙasar Panama da ya toshe hanyar a jiya Litinin. An nuna yadda aka kawar da jirgin daga hanyar kai tsaye da gidajen talabijin lamarin ya fuskanci yabo da kuma jinjinawa.

Rahotanni dai sun bayyana cewar a kowace ranar mashigar tana yin asarar kuɗaɗen da suka kai Dala miliyan 14-15 a kowace rana sakamakon tsaikon wannan jirgin saboda kasancewar kashi 15 cikin ɗari na kayayyakin da ake jigilansu a duniya suna bi ta wannan mashigar ne.

342/